<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 (Kira da Amsa)
 K : Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko duka ne,
 A :   Yesu shi sarki ne, Sarkin Sarakuna.

[V2]
 K :  Ya bar sarauta a can cikin sama,
 A:     Ya zo a duniya a cikin talauci,

[V3]
 K:  Ya sha wahala a gun Yahudawa
 A:     Har suka yi shawara, suka giciye shi.

[V4]
 K:  Ya yi mutuwa fa, mutuwa ta giciye,
 A:    Ya zubda jinisa domina ya panshe mu.

[V5]
 K:  Bayan kwana uku sai Yesu ya tashi.
 A:     Yesu ya ci nasara, nasara ta mutuwa.

[V6]
 K :  Ku fa mutane, ku zo fa mu tuba,
 A :     Mu bi Yesu Mai Nasara da mutuwa.

[V7]
 K :  Sai fa, mu bi Shi da zuciya ɗaya
 A :     Gama babu ceto sai wurin Yesu fa.

[V8]
 K:  Ku zo maza mutane ku zo maza mu tuba
 A:     Yesu ya hau sama yana shirya wuri.

[V9]
 K:  Za ya sake zuwa domin masu-binsa.
 A:     Lalle akwai murna ran da mun kai sama.

[V10]
 K:  Yesu mun gode domin mutuwarka.
 A:     Yesu mun gode domin kai, ka tashi.

[V11]
 K:  Karɓi sarauta da iko da girma.
 A:     Taka ce har abada, har abada abadin.</lyrics>
<title>Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko Duka Ne LW586</title>
<hymn_number>586</hymn_number>
</song>